A yayin da ake ci gaba da ce-ce ku-ce dangane da batun nan da mai martaba Muhammadu Sanusi na biyu, yayi akan zamatakewan ma’aurata da batun nan na rama duka ga mazajen da ke dukan matansu, akan haka ne muka ji ta bakin wasu mata na shin ko zasu iya rama duka ga mazajen masu duka, inda muka sami ra’ayoyi mabanbanta.
Amina cewa tayi ba zata iya ramawa ba idan har mijinta ya doke ta, a cewarta hakan ba tarbiyar ‘yar Malam Bahaushe bane, illa ta yi hakuri tare da kai kararsa wajen hukuma da zarar dukan yayi yawa ko ta hakura da auren.
Aisha kuwa cewa tayi hukunci yayi saboda a cewarta babu dalilin da miji zai daga hannu ya duke matarsa .
Hadiza Suleman kuwa cewa tayi a farko zata yi hakuri amma idan tafiya tayi tafiya ya ci gaba da dukanta to lallai zata rama , idan ya duke ta a ciki to ita ma a nan zata doke shi domin jiki bai fi jiki ba.
Wata dattijiya Malama Aisha Yakubu tace a wancan lokacin da wuya a samu miji mai dukan matarsa, hasalima idan miji na tsawatawa to matar kan sunkuyar da kai domin girmamawa.