Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra’ayoyin Mutanen Najeriya Kan Dage Babban Zabe.


Najeriya Zaben 2015 Buhari Jonathan
Najeriya Zaben 2015 Buhari Jonathan

Jama’a dai na ta bayyana albarkacin bakinsu kan matakin da hukumar zabe ta dauka na dage zabubbukan da ta shirya zuwa wani lokaci nan gaba.

A yayin da wasu ke ganin dage zaben yayi dai dai, wasu kuwa gani suke hukumar zaben bata kyauta ba. Wasu mutane dai na ganin dalilin hukumomin tsaro na ganin bazasu iya tabbatar da yin zabe cikin kwanciyar hankali ba, ba dalili bane kasancewar sun san da zuwan zaben, amma basu dauki wani kwakwkwaran mataki ba na dalikile ko kuma kawo zaman lafiya a kasar.

A cewar baraden lafiya Alhaji Musa Liman Kwande, cewa yayi dage zaben na kan ka’ida, “inda jami’an tsaro ne suka bada hujja, cewa bazasu iya kare hakkin jama’a da dukiyar jama’a ba a wannan lokaci, hankali ya tattara a Yobe, Borno, Adamawa da Gombe, shi kuma aikin tsaron kasa duk wanda kabai wa aikin tsaro yazo ya baka labarin halin da gidan, garin ka ko kasarka ke ciki to dole ne ka karbi shawarar sa, muddin baka karbi shawarar suba to kuwa zakayi dana sani.”

Shi kuma Musa Goji cewa yayi jama’a suyi hakuri su bar kome ga Allah, “Mutane suyi hakuri domin komai nufin Allah ne, abubuwan da suka faru a baya missali in mutum ya saurari maganar Abdulsalam a safiyar jiya Lahadi, zai gane cewar shugabannin mu iyayenmu ma sun gane cewar a barwa Allah da nufin sa, idan mai gadi na tsaron kofa, kai me gida zaka fito yace ka koma ciki in har baka koma ba abinda ya sameka kai ka jawowa kanka, muyi hakuri mu bar komai ga Allah.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG