Pep Guardiola, na Manchester, City, ya lashi takobin cewa ba zai sake sanya dan wasan gaba kuma dan kasar Ivory Coast, Yaya Toure, a wasani da Manchester City, zata bug aba har sai shi, Yaya Toure yana nemi gafara daga kungiyar ta Manchester City, a bisa kalaman wakilinsa.
Wakilin Toure, Dimitri Seluk, ya zargi Pep Guardiola, da cewa ya yi watsi da Toure, tun daga fara gasar lig din zakaru a wannan watan na Satumba.
Da yake ganawa da manema labarai Guardiola, ya ce tun daga lokaci da Dimitri, yayi wannan kalamin yayi waje da Yaya Toure, sai idan Dimitri, ya koma ya tara manema labara ya nemi gafara da kungiyar Manchester City.
Ya kara da cewa yin hakan ne kwai zai baiwa Yaya Toure, damar sake samun damar kasancewa ana sa shi a wasani kungiyar.
Guardiola,ya ce “a matsayi na Koch bazan amince da kowane wakilin dan wasa idan hard an wasan sa bai samu an sa shi ya buga was aba ya kasance zasu ruga ga manema labarai ba.