An shirya wani wasan kwallon kafa na sada zumunta tsakanin kungiyoyin kwallon kafa na jamiyyar PDP, da na APC, a jihar Gombe.
‘Ya’yan jamiyyar PDP, ne suka shirya wannan wasa na sada zumunta domin murnar cikar jihar Gombe, shekaru ashirin da kafuwa.
Muhammad Adamu Yayari, wani dan jamiyyar APC, ya yaba da wannan hangen nesa da kungiyar PDP, ta yin na shirya wannan zumuncin, ya na mai cewa wannan ya nuna cewar siyasa ba gaba bace.
Ya kuma yi kira ga sauran jihohin Najeriya, da suyi koyi da abinda jihar Gombe, tayi ta hanyar kirkiro abubuwan da zai hada zumunci tsakaninsu da ‘yan adawa a jihohinsu.
Shima Malam Salisu na kungiyar PDP, ya ce wanna abin a yaba ne kamar yadda ‘yan APC, suka amsa gayyatar daga yanzu za’a tabbatar da ganin cewa duk wani abin da ya taso a gwamnatance ya zama wajibi APC, ta kasance a ciki.
Kungiyar kwallon kafa ta PDP, dai ta doke kungiyar kwallon kafa ta APC, da kwallaye biyu da nema.