Alhaji Jibril Al-Walid sakataren kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP yace zaben da aka gudanar a jihar Nasarawa, wato jiharsa, ya bashi tsoro. Yace daga sakamakon da aka fitar jam'iyyar APC ta ba kantu kananan hukumomi shida yayin da ta baiwa PDP hudu. Yace bai san dalilin da suka bayar ba kan yadda suka yi rabo kamar an raba kosai. Yace yankunan da suka fi samun tashin hankali suka baiwa PDP kamar Nasarawa Eggon ,Keffi, Kokona da makamantansu. Hatta mahaifar Alhaji Abdullahi Adamu PDP ta ci wato komawarsa APC bata da ma'ana ko anfani.
Dangane da yadda PDP ta samu hukumomi hudu wakilin Muryar Amurka yace ai yakamata a ce PDP tana murna. Sai Sanata Walid yace kwace aka yi masu domin haka ba batun yin murna ba ne. Yace an karbe masu ne da karfi da yaji amma APC ba zabe ta ci ba. Yace yadda mutane ke fita daga APC suna dawowa cikin PDP babu yadda za'a ce kananan hukumomi hudu kawai suka ci.
Idan an bi gaskiya inji Sanata Al-Walid PDP zata tashi da hukumomi 12 ta bar APC ta shida kawai. Kan ko PDP na son yin anfani da rinjayenta a majalisar dokokin jihar ta tsige gwamnan ta sa mataimakinsa Damishi Luka wanda ya koma PDP bayan APC ta koreshi sai Al-Walid yace haki ne na 'yan majalisa domin su ne suka san laifin da yayi amma su a matsayinsu na iyaye saidai su bayarda shawara. Yace tunanin tsige gwamna bai zo masu ba tukunna. Yace idan an gaya masu zasu dubi abubuwa su bada shawara yadda ya kamata .
Garahoro.