Dan wasan gaba na kungiyar Juventus, Paulo Dybala, mai shekaru 25 da haihuwa dan kasar Agentina ya bayyana cewa bashi da burin barin kungiyarsa ta Juventus, duk da rade radin da akeyi na cewa yanason komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester City dake kasar Ingila.
A kwanakin baya dai an alakanata dan wasan da komawa kungiyar ta
Manchester City, bayan da shugabannin kungiyar na City suka ce zasu tuntubi Juventus akan sayan dan wasan.
Sai dai dan wasan yace yana jin dadin zama a kungiyarsa ta Juventus, kuma bashi da ra'ayin barin kulob din, don zuwa wata kungiya kamar yadda mutane suke rade radi, inda yace shima haka yake gani a mujallu.
Dybala ya kara da cewar, Juventus kungiya ce wadda take da burin ganin tazama zakara a duk duniya kuma nima shine burin dake gabana.
Facebook Forum