Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paraguay Ta Bude Ofishin Jakadanci a Birnin Kudus


Shugabannin Kasashen Paraguay Da Isra'ila
Shugabannin Kasashen Paraguay Da Isra'ila

Kasar Paraguay ta bude sabon ofishin jakadancinta a birnin Kudus yau Talata, inda ta zamo kasa ta uku da ta yi wannan yunkurin mai kunshe da siyasa a cikin satin da ya gabata.

Shugaban kasar Paraguay Horacio Cartes, a jawabin bude ofishin, ya bayyana cewa dauke ofishin jakadancin daga TelAviv zuwa Birnin Kudus na da dumbin tarihi kuma zai karfafa dangantaka tsakanin Isra’ila da kasar ta Paraguay.Frayim-ministan Isra’ila Benjamin Nethanyahu yayi maraba da wannan shawarar.

A satin da ya gabata ne Amurka ta kasance kasa ta farko da ta bude ofishin jakadanci a birnin Kudus inda ta cika alkawarin da shugaban kasar Donald Trump yayi a lokacin yakin neman zaben shi. Guatamela ta biyo sahun Amurka bayan kwanaki biyu.

Falasdinawa sun fusanata ainun da hakan, domin suna ganin gabashin Birnin na Kudus a matsayin babban birnin kasar ta Falasdinu a nan gaba, a yayin da su kuma Isra’ilawa ke ganin Birnin Kudus a matsayin babban birnin su mara rabuwa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG