Ruwan sama mai yawa da kuma fashewar da wata madatsar ruwa ta yi a jihar Borno sun haddasa mummunar ambaliyar ruwa a Maiduguri, lamarin da ya sanya ruwa ya shanye gidaje da ma’aikatu da sauransu a birnin. Gwamnatin kasar ta sha alwashin taimakama wadanda ambaliyar ta shafa.