Bayanan dake fitowa daga takardun da aka gano a gidan Osama Bin Laden a Pakistan bayan mutuwarsa a bara, sun yi nuni da mawuyaciyar dangantakar da ake samu a wasu lokuta a tsakanin uwar kungiyar al-Qaida da kuma rassanta.
Takardun da cibiyar yaki da ta’addanci a kolejin horasda sojoji ta Amurka da ake kira West Point ta fito da su jiya alhamis, wadanda kuma wasiku ne, sun nuna shugaban na al-Qaida cike da bacin rai na irin dabarun da kungiyoyin jihadi a Gabas ta tsakiya, da Afirka ta Arewa suke amfani da su, da kuma yadda ya kasa maida su karkashin umurninsa.
Daya daga cikin wadanda suka yi wannan nazari, Nelly Lahoud, tace wasikun sun nuna kamar sabbin kungiyoyin suna so su fi karfin Bin Laden. Lahoud tace Bin Laden yana son kungiyoyin su fi maida karfinsu kan Amurka, kuma ya nuna fushinsa kan hare hare da suke kaiwa da suke sanadin mutuwar musulmi.
Haka kuma Bin Laden yayi kakkausar suka kan wasu ma abuta jihadi kamar marigayi dan Amurkan nan Anwar al-Awlaki, wanda Amurka ta kashe bara a Yemen da jirgin nan da bashi da matuki, haka kuma bai ji dadin Kungiyar Taliban ta Pakistan. Bin Laden yayi watsi da dai-daikun mutane dake kai hare hare na kashin kansu.