Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta bayyana sunan Ole Gunnar Solskjaer, a matsayin sabon kocin kungiyar mai rukon kwarya zuwa karshen kakar wasa na bana. Kocin ya maye gurbin Jose Mourinho da ta sallama a ranar Talata da ta gabata sakamakon rashin samun cigaba da kungiyar batayi ba, musamman a firimiyar Ingila.
Ole Gunnar Solskjaer, mai shekaru 45 da haihuwa, tsohon dan wasan Manchester United ne a shekarun baya da suka wuce dan kasar Norway, ya shafe kakar wasanni 11 tare da Manchester a karkashin jagorancin Sir Alex Ferguson, inda ya zurara kwallaye 126 a wasannin da ya buga mata.
Bayan haka kuma shi ya taimaka wajan sanya kwallon da ta ba kulob din nasarar lashe gasar zakarun Nahiyar Turai a shekarar 1999, inda ta doke Bayern Munich a Nou Camp.
Kafun nadin nasa Solskjaer, ya kasance mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Norwegian Molde, dake kasar Norway inda a watan da ya wuce ya sabunta kwantirakinsa da kungiyar.
Kocin zai yi aikine tare da Michael Carrick da Kieran McKenna, wanda sukayi aiki da tsohon kocin Mourinho.
Shugaban Kungiyar ta Manchester United Ed Woodward, ya bayyana sabon kocin Solskjaer, mai rukon kwarya a matsayin tsohon dan wasan kulob din, kuma mai kishin kungiyar wanda zai kawo sauyi mai amfani a yayin zamansa a wajan.
Wasan farko da zai fara jagoranta a kungiyar a ranar Asabar mai zuwa tsakanin Manchester da Cardiff City. Manchester United tace zata sanarda sunan kocinta na din-din-din zuwa karshen kakan wasan bana.
Facebook Forum