Jami'in dake kula da alamuran al'adu na ofishin jakadancin dake Abuja ya kaddamar da reshen Kano na dandalin.
Yace alfanun musayar dalibai da sauran harkokin bada horon ilimi shi ne yaukaka dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka.
Yace 'yan Najeriya na zagaya biranen Amurka daban daban domin yin karatu da yin nazari a jami'o'i da cibiyoyin ilimi lamarin dake basu damar fahimtar Amurka da jama'arta.
Haka ma Amurkawa na samun kyakyawar fahimta kan al'adu da sauran muhimman alamura da suka shafi rayuwar 'yan Najeriya.
Makasudin kaddamar da dandalin shi ne yanzu 'yan Najeriya da suka yi karatu a Amurka suka kuma dawo gida zasu iya fadakar da matasa ta hanyar anfani da abubuwan da suka koyo na ilimi dangane da Amurka.
Dr Abdullahi Maikano Madaki na jami'ar Bayero Kano yana cikin wadanda suka yi karatu a Amurka yace anfani dandalin shi ne su fitar da wasu tsare tsare tare da jajircewa domin taimakawa al'umma.
Farfasa Mahmud Lawal da ya gabatar da mukala a taron kaddamar da dandalin yace yana da alfanu ta fannoni da dama.Dandalin zai ba matasa da suke son yin karatu a Amuraka su fahimci abubuwan da zasu fuskanta a kasar.
Ga karin bayani.