Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Zai Hau Kujerar Na Ki Kan Dokar Hana Karbar 'Yan Gudun Hijira daga Syria


Kakakin Majlisar Wakilan Amurka Paul Ryan
Kakakin Majlisar Wakilan Amurka Paul Ryan

Duk da cewa majalisar wakilai tare da goyon bayan wasu 'yan Democrat sun amince da dokar hana shugaba Obama karbar 'yan gudun hijira daga Syria da Iraqi, shugaban yace zai hau kujerar na ki

Majalisar wakilai ta Amurka ta amince da kudurin da zai dakatar da shirin shugaba Barack Obama na bada mafaka ga 'yan gudun hijira daga Iraqi da Syria su dubu 10 cikin kasa nan zuwa badi. Amma Mr. Obama yayi alkawarin ba zai amince da dokar ba idan har ta sami amincewar majalisar dattijai.

Shugaba Obama yana ganin shirin nasa na tsugunar da wadannan mutane zai ci gaba kamar yadda ya tsara. Shugaban na Amurka yace bayan da aka gama surutai aka samu natsuwa, aka dubi gaskiyar magana, shirin zai ci gaba. Shugaban ya bayyana haka ne yayinda yake halartar taron koli na kungiyar kasashe dake yankin Asiya da Pacific a Manila na kasar Phillipines.

Wakilai 289 suka goyi bayan kudurin 137 kuma suka ki, galibin wakilai 'yan Republican da kuma wasu da dama daga jam'iyyar Democrat ta Mr. Obama ne suka goyi bayan yunkurin tsaurara bincike kan 'ayn gudun hijirar da zasu shigo Amurka. Babu tabbas kan yadda kudurin zai kaya a majalisar dattijan Amurka.

Wasu wakilan sun bayyana damuwar 'yan ta'adda zasu saci jiki su bi 'yan gudun hijira su shigo Amurka su aikata ta'addanci shigen dai abunda ya faru a birnin Paris na kasar Faransa ranar Jumma'a ta makon jiya.

Amma shugaba Obama yace ana yiwa 'yan gudun hijira "bincike mai tsanani," kamin a kyale su shigo Amurka, daga nan yayi watsi kan ikirarin da ake yi cewa shigarsu zai kasance babban barazana ga tsaro.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG