Shugabannin Afirka sun zabi ministar harkokin cikin gidan Afirka ta Kudu, Nkosazana Dlamini-Zuma, a zaman sabuwar shugabar Kungiyar Tarayyar Afirka, ta zamo macen farko, kuma 'yar Afirka ta Kudu ta farko da ta taba rike wannan mukami.
Dlamini-Zuma ta doke shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka mai ci, Jean Ping, bayan zagaye hudu na jefa kuri'a jiya lahadi a wurin taron kolin kungiyar a Addis Ababa a kasar Ethiopia.
Ita ce tsohuwar matar shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma.
A can baya, wannan mukami na shugabancin Kungiyar Tarayyar Afirka ya kan fada hannun wani jami'in gwamnati daga wata karamar kasa a nahiyar ne. Dlamini-Zuma ta ce babu wata alaka a tsakanin fitowarta daga babbar kasa kamar Afirka ta Kudu da kuma wkadayinta na bayar da gudumawa ga Kungiyar.
Kungiyar Tarayyar Afirka tana takalar wasu fitinu a sassan nahiyar. Tana nazarin yiwuwar tura sojoji domin su yaki 'yan tawaye dauke da makamai a kasar Kwango-ta-Kinshasa. Har ila yau tana goyon bayan shirin kasashen Afirka ta Yamma na yakar masu kishin addini a yankin arewacin kasar Mali.