Lura da yadda ake fuskantar durkushewar kamfanonin da ke ayyukan hako ma’adanai a yankin arewacin kasar Nijar, ya sa kungiyar ma’aikatan ma’adanai ta Syntramine kiran wannan babban taro da nufin bullo da shawarwarin da zasu taimaka a sami mafita, a cewar sakataren kungiyar mai barin gado Moutari Aboubakar.
Rashin mutunta ‘yancin ma’aikata da rashin bin ka’idodin ayyukan hakar ma’adanai na daga cikin matsalolin da suka dauki hankalin mahalarta wannan taro.
"Halin da ake ciki a yankin da ake gudanar da ayyukan hakar ma’adanai wani abu ne da ke bukatar saka ido sosai, saboda haka ya zama wajibi hukumomi su karfafa matakai domin bin diddigin wannan al’amari." inji Moutari Aboubakar.
A karshen wannan taro shugabanin kungiyar Syntramine zasu gabatarwa gwamnati takardun shawarwarin da suke gani zasu taimaka wajen magance matsalolin da ke hana ruwa gudu wajen tafiyar da sha’anin albarkatun karkashin kasa ta yadda kasar da jama’arta zasu ci moriyar wannan arziki da Allah ya ba su.
A saurari cikakken rahoton cikin sauti daga Yamai:
Facebook Forum