Rahoton dake rubuce cikin shafuka goma sha daya ya yi cikakken bayani akan yadda binciken ya gudana a karkashin shugaban kungiyar kare hakin dan Adam Farfasa Khalib Ikilib.
'Yan kwamitin sun kwashe watanni uku suna sauraron shaidu da wadanda aka zarga da haddasa abubuwan da suka faru a yayin zanga zangar daliban Jami'ar Yamai ranar goma ga watan Afirilu.
Yan kwamitin sun ziyarci wuraren da aka yi batakashi tsakanin dalibai da jami'an tsaro abun da ya bada damar gano cewa kowannensu ya sabawa doka.
Kakakin kwamitin Mamman Sanusi Bukari Hamidu yana mai cewa kiran da daliban Jami'ar Yamai suka yiwa sauran daliban dake ciki da kewayen Yamai ba ya kan ka'ida. Haka 'jami'an tsaro sun bannata kayan kasa da na dalibai suna ta bugun duk wanda suka gani a jami'ar.
Dangane da mutuwar dalibin da rikicin ya rutsa dashi lamarin da ya haddasa zazzafar muhawara tsakanin dalibai da gwamnatin kasar, kwamitin ya tuntubi ma'aikatan asibiti masu binciken gawa da 'yansandan yankin bincike.
Inji kakakin kwamitin likitan da ya binciki gawar yace wani abu ne ya bugeshi a kansa. Su ma 'yansandan dake bincike sun ce dalibin ba faduwa ya yi da kansa ba ya mutu. Wani abu ya buga mashi kai.
A gaban dalibai aka gabatar da rahoton kwamiti din kuma sun bayyana gamsuwarsu da rahoton. Muftau yace rahoton ya karyata abun da hukuma ta ce tun farko. Rahoto ya tabbatar 'yansanda ne suka kashe dalibin, danuwansu. Daliban zasu duba su gani ko zasu kai kara domin samar ma dalibin hakkinsa. Inji daliban yanzu ya kamata a kara bincike a gano jami'in tsaron da yayi harbin da ya kashe dalibin.
Rahoton da aka mikawa Firayim Ministan kasar ya bada shawarwari akan yadda za'a gujewa sake aukuwar irin abun da ya faru.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Facebook Forum