Dan wasan kasar Croatia mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Ivan Rakitic, ya ce yana da yakinin nan gaba kadan dan wasan gaba na Kungiyarsu ta Barcelona Neymar, shi zai gaji Lionel Messi; a matsayin gwarzon kwallon kafa na duniya (World Best) Bisa lura da irin rawar gani da yake takawa a fagen tamola a duniya kama daga kasarsa ta Brazil da kuma Kungiyarsa ta Barcelona.
Neymar dai ya taho Barcelona ne a shekara ta 2013, daga Kungiyar kwallon kafa ta Santos na kasar Brazil, inda ya fafata wasanni har guda 149, wa kungiyar ta Barcelona, ya kuma zurara kwallaye 90 a raga.
Neymar zai buga wasansa na 150 a Barcelona a gobe a wasan da zasuyi da Manchester City a gasar cin kofin zakarun turai na bana.
Rakitic ya ce ya na kaunar Cristiano Ronaldo, domin babban dan wasane amma idan ana zancen gwarzone to sai Messi me gadonsa kuma Neymar ne.
Shi kuwa tsohon dan wasan Real Madrid, Roberto Carlos ya ce babu wanda ya dace da ya zamo zakaran kwallon kafa na duniya a bana irin Cristiano Ronaldo, bisa irin nasarorin da ya samu ta fagen kwallon kafa a bana kama daga Kungiyarsa ta Real Madrid.
Wanda ya jagoranci kasarsa wajan samun nasarar cin kofin zakarun nahiyar turai 2015/2016.