Dan wasan gaba na kungiyar Paris-saint German Neymar, ya musanta rade radin da akeyi akansa, na cewar yanzu yafi maida hankalinsa wajen shirya bukukuwan casu, fiye da cimma burinsa na shiga sahun gwarzon 'yan wasan kwallon kafa a duniya.
Neymar, yanzu haka yana jinya na tsawon makwanni 10, sakamakon raunin da ya samu a kafarsa cikin watan Janairu da ya gabata, amma ya shirya gaggarumin bukin murnar cikarsa shekaru 27, da haihuwa wanda akayi a birnin Paris.
Hakan ya janyo kace nace inda wasu ke sukarsa, da tunanin ko dan wasan zai iya jagorantar PSG zuwa matakin nasarar da take son kaiwa na lashe gasar Zakarun Turai, la’akari da cewa yawan yin bukukuwa da shaye-shaye kan shafi kwazon dan wasa.
Kamar yadda aka ruwaito cewa, hakan na daga cikin musabbabin abubuwan da suka dushe tauraron tsohon gwarzon kwallon kafa na duniya Ronaldinho.
Neymar, ya ce rayuwar sa ta yau da kullun ta sha babban da rayuwarsa a
fagen kwallon kafa, don haka babu bangaren da zai shafi kowanne domin hanyar wasa daban hanyar Casu itama daban.
Facebook Forum