Yau Laraba, yara 'yan makaranta a Afrika ta kudu su miliyan goma sha biyu ne suka raira wakar taya Nelson Mandella, tsohon shugaban Afrika ta kudu, gwarzon yaki da mulkin wariya, murnar cika shekaru 94 a duniya.
Mr. Mandela wanda ya yi murabus daga ayyukan gwamnati, ya wuni tare da iyalinsa a gidansa dake kauyen Qunu. a kudu maso yammacin kasar.
A halin da ake ciki kuma, mutane a duk fadin duniya suka yi mintoci 67 Laraban suna gudanar da ayyukan sa kai na tallafawa masu bukatar taimako. Hakan na nufin minti daya a kan kowacce shekarar da ya shafe yana aikin gwamnati.
Mr. Mandela ya zama shugaban Afrika ta Kudu, bakar fata na farko a alif dari tara da casa’in da hudu, bayan ya shafe shekaru 27 a gidan yari, a saboda gwamnati wancan lokacin ta same shi da laifin yaki da gwamnatin tsirarru ta nuna wariyar launin fata.