Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neja: Shin Ina Batun Tashar Jiragen Ruwa Ta Baro?


Wani jirgin ruwa a kasar Amurka
Wani jirgin ruwa a kasar Amurka

Bayan share kimanin shekara daya da rabi da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bude tashar jiragen ruwa ta garin Baro a jihar Neja har ya zuwa wannan lokaci babu wani abu da ke gudana a tashar.

Al'amarin da yasa al'ummomin jihohin Neja da Kogi da Kwara ke cewa suna cike da damuwa matuka domin kuwa hatta hanyar motar zuwa garin na Baro ba ta da kyau.

Baba Muhammad Dzukogi shine shugaban wata gamayyar kungiyoyin matasa masu neman hadin kai da cigaban al'umma wanda kuma ya jagoranci taron manema labarai akan lamarin tashar ruwan Baron, ya kuma ce "hatta garin na Baro ya zama kamar wani gari da yaki ya ci saboda haka akwai bukatar hukumomin Najeriya su mayar da hankali akan tashar Baron".

A nasu bangaren, wadansu daga cikin shugabannin kungiyoyin matasan da suka halarci taron manema labaran sun nuna damuwa da rashin hanya mai kyau zuwa Baron saboda haka sun bayyana bukatar ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wani abu cikin hanzari akan lamarin.

Da yake maida martani, kakakin shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya sheda wa Muryar Amurka cewa a baya yayi magana da shugaban kasa akan lamarin Baron amma tunda aka fara batun korona baiga shugaban kasa ba.

A cewarsa tabbas batun Baro yana nan kuma zai kara matsa kaimi akan lamarin.

Saurari wannan rahoton cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG