WASHINGTON, DC —
Najeriya, zata wakilci Afirka, a gasar kwallon kafa na gabar teku, na duniya wanda za’ayi a Bahamas.
Najeriya, ta sami wakilicin ne bayan da ta lallasa kasar Morocco, da ci shida da daya a wasan kusa da na karshe a gasar kwallon gabar teku na cin kofin kasashen Afirka, ranar asabar din da ta gabata.
Abu Azeez, ya jefawa Najeriya, kwallaye biyu,Emmanuel Owhoferia, Suleiman Ogodo da Emeka Ogbona suma sun jefawa Najeriya kwallaye a ragar Morocco. Sami Lazal, ne ya jefawa Marocco kwallo daya tilo da ta samu.
Sau hudu Najeriya ke samun nasaran buga gasar kwallon kafa na gabar teku na duniya, inda a shekarar 2007 da 2011 , ta kai sagayen kusa da na karshe.