Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Aka Gayyaci Najeriya Taron G20


Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Nerandra Modi, Firam ministan India
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Nerandra Modi, Firam ministan India

Biden ya yi ƙira da a sanya Najeriyar cikin mambobin ƙungiyar kasashen ta G20.

Shugaban Amurka Joe Biden, ya jinjinawa takwaran aikinsa na Najeriya Bola Ahmed Tinubu, bisa salon jagorancinsa, inda ya kwatanta kasar a matsayin jagora a ɓangaren dimokraɗiyya da kuma ƙarfin tattalin arzikia Nahiyar Afirka.

Kazalika ya yi ƙira da a sanya Najeriyar cikin mambobin ƙungiyar kasashen na G20.

Ƙungiyar mai mambobi 20 na ƙasashen da suka ci gaba da kuma ƙasashe masu tasowa da ake musu lakabi da G20, an kafa ta ne a shekarar 1999 da zimmar shawo kan matsalolin tattalin arziki da mambobin ƙungiyar suka fuskanta a shekarun baya.

Ƙungiyar na taron ƙarawa juna sani sau ɗaya a duk shekara, inda mambobin da suka haɗa da ƙasar Amurka da kuma sauran ƙasashen nahiyar Turai, Asiya da kuma Afirka ta kudu wanda ita kaɗai ce mamba a nahiyar Afirka.

Mambobin na G20, sun gudanar da taron su na18 bana a ƙasar Indiya mai taken "Ƙasa Ɗaya, Al'umma Ɗaya, Da Kuma Ci gaba Bai-Ɗaya."

A taron nata, ƙungiyar ta gayyaci Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, wanda ba ya daga cikin mambobin ƙungiyar ta G20, kuma ya samu ganawa da Shugabannin ƙasashe da dama, ciki har da Shugaban Amurka Joe Biden.

Bayan ganawar tasu, Fadar White House ta wallafa bayanin Shugaba Biden, inda aka ji yana jinjinawa Shugaban na Najeriya, bisa irin jajircewarsa wajen ganin ɗorewar dimokraɗiyya a nahiyar Afrika.

Shugaba Biden, ya ce Najeriya ce jagora a bangaren dimokraɗiyya a nahiyar, bisa irin namijin kokari da take yi don ganin mulkin dimokraɗiyya ya dawo a Jamhuriyar Nijar.

Shugaban na Amurka, ya ƙara da cewa Najeriya ce kan gaba a fannin tattalin arziki a nahiyar, ya kuma kira da a sanya ta cikin mambobin na G20.

A hirarsa da Muryar Amurka, Ambassada Dahiru Suleiman, tsohon jagora na samar da zaman lafiya a ƙasar Sudan, ya ce wannan gayyata da aka yi wa Najeriya amma yi jinkiri domin Najeriya ƙasa ce da ya dace tuntuni tana cikin irin wannan ƙungiya.

Dakta Isa Abdullahi, Masanin tattalin arziki ne a Jami'ar Tarayya da ke Kashere, y ace Amurka ta yi la'akkari da yadda karfiin tattalin arzikin Najeriya yake a nahiyar da kuma sabbin tsare-tsaren da ta zo da shi a fannin ne ya sa Amurka take son shigarta cikin jerin membobin G20.

Sai dai Najeriya na fuskantar ƙalubale daga ƙasashe takwarorinta wajen shigarta cikin jerin mambobin ƙungiyar G20, ganin irin karfin ikonta da kuma girman tattalin arzikinta a nahiyar Afirka.

Saurari rahoton Ruƙayya Basha:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG