Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta shawarci ‘yan kasar da ke shirin tafiya zuwa kasar Australia da su sani cewa akwai biranen kasar dake fama da tabarbarewar tsaro.
Cikin sanarwar da mukaddashin mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Mr. Kimiebi Imomotimi Ebienfa yace “ Bisa lura da rahotannin nuna wariya, cin zarafi da zagin baki ‘yan kasashen waje, kyamar musulmai ya zama wajibi mu sanar tare da nunawa dukkan masu shirin tafiya koma ‘yan Najeriya dake zaune a kasar Australia hatsari da zasu iya fuskanta na yiwuwar barkewar rikici a wasu birane.”
A farkon watan Disambar shekarar 2024 dai an sami hare-haren kin Musulmai da ma Yahudawa a wani kauye da ke gefen birnin Sydney.
Wannan gargadi na zuwa ne sa'o'i bayan da kasar Australia ta yi wa ‘yan kasarta gargadi kan su guji yinkurin zuwa Najeriya saboda matsalar tsaro.
Ma’aikatar harkokin wajen ta Najeriya ta bukaci ‘yan kasar da su kasance masu taka tsantsan da lura.
Sananan idan sun fuskanci musgunawa ko nuna wariyar launin fata su gaggauta sanar da ofishin jakadanci Najeriya da ke Canberra, Australia.
Dandalin Mu Tattauna