Kawo yanzu dai kasashen biyu suna kasuwanci akan magunguna ne na dala miliyan dari kowace shekara abun da mahukuntan Najeriya suka ce yayi kadan kwarai da gaske. Dalili ke nan suke taron yini biyu tsakanin masu sarafa magunguna na Najeriya da na Pakistan.
Daya daga cikin shugabannin taron na Najeriya Ibrahim Ahmed Yakasai yace an zabi kasar Pakistan ne saboda kwarewarta a fannin magunguna. Dalili na biyu shi ne kasar tana da yanayi iri daya da na Najeriya.
Akan dalilin da yasa ba zasu yi kokarin bunkasa masana'antun sarafa magunguna na gida ba sai Ahmed Yakasai yace yin taron da Pakistan domin a tada na gida ne. Yace idan sun kawo kayansu ko kudinsu ko kwakwalwarsu su hadu da albarkatun da Allah Ya baiwa Najeriya domin su tashi tare.
Ahmed Yakasai yace zasu tabbatar mutane da suka gayyato ba zasu fada hannun miyagun mutane ba. Za'a yi hulda ne da mutane masu mutunci da halin arziki.
Wani dan kasar Pakistan Ahmed yace ya yadda ya zo Najeriya shiga yarjejeniyar yace Najeriya kasa ce mai albarka da wadatacciyar kasuwa da mutum zai iya saka jari ya kuma samu fita. Su 'yan Pakistan din da zasu shigo zasu sarafa magungunan ne a cikin kasar ta Najeriya.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.