Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na Duke Tsohon Ciniki na Samar da Manfetur Nagarttace


Noma
Noma

Na duke tsohon ciniki, yawaita dogaro da akeyi da manfetur nada matukar illa ga tattalin arzikin kasa a ko ina a duniya, masu bincike sun gano wasu hanyoyi da dama da za’a iya sarrafa albarkatun gona don samar da man fetur wanda zai samar da ingantatun rayuwar. Ta bakin Farfesa Baba Jibirin Zowo, man fetur da ake samowa daga cikin karkashin kasa na da illoli da dama wanda suka hada da gurbata iska da al’uma ke sha'ka don gudanar da ingantaciyar rayuwa.

Hanyar da yakama ta a bin don magance wannan matsalar da kuma taimakama tattalin arzikin kasa shine, a koma ma harkar noma, wanda za’a iya samar da albarkatun gona kamar su rake, dawa, masara da dai sauransu wanda za’a fitar da abinci a ciki kuma a samar da man fetur duk a ciki, wanda za’a samu riba hudu, na farko a samu abinci, na biyu a samu nagartacen tattalin arziki, na uku a samu ingantatun muhallai, kana na hudu a samu biyan bukata musamman ma a motoci, jirage, ko ingina bada wuta.

Don haka yakamata al’uma su koma gona wanda sanin kowane a Arewacin Najeriya kowa yasan su da noma, to lallai yanzu yakamata mutane su duba wannan bangaren don samar da rayuwa me nagarta. Kuma al’uma su sani wannna wata damace wadda mutane zasu kara samun ilimi don kere-kere ko kir-kiran wasu abubuwan da za suyi dai-dai da zamani.

Wanda idan aka duba za’aga cewar abun da ke taimaka ma kasashen da suka cigaba kenan, wajen bincike da kuma aiwatar da wannna binciken wajen morema rayuwa da fitar da wadannan kayan zuwa kasashen waje wanda tananne kasa zata samu kudin shiga.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG