Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Biyu Suna Kan Gaba a Zaben Afghanistan


 Abdullah Abdullah tsohon ministan harkokin wajen kasar Afghanistan wanda ke kan gaba kadan a zaben shugaban kasa
Abdullah Abdullah tsohon ministan harkokin wajen kasar Afghanistan wanda ke kan gaba kadan a zaben shugaban kasa

Yayin da ake cigaba da kirga kuri'u a zaben da aka yi a kasar Afghanistan mutane biyu suna kan gaba lamarin da ka iya kaiga zagaye na biyu

A Afghanistan mutane biyu sune suke kan kan gaba a zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar biyar ga wannan wata. Mutanen sune tsohon ministan kudi Ashraf Ghani da kuma dan hamayya Abdullah Abdullah.

A yayinda aka kidaya kashi 10 daga cikin dari na kuri’aun da aka kada, Abdullah ya sami kusan kashi 42 daga cikin dari na kuri’u da aka kada. Shi kuma Ashraf Ghani ya sami kashi 38 daga cikin dari. Dan takara na uku Zalmai Rassoul yana can baya da kashi 10 daga cikin dari na kuri’un da aka kada.

Abdullah ya gayawa kamfanin dillancin labarum Associated Press cewa ya tattauna da Zalmai Rassoul. Duk da haka yace za’a garaje ga dami idan aka fara maganar yiwuwar kulla kwance. Yace idan har Allah yasa ya samu nasara, to zai kafa gwanatin hadi kan kasa.

Kimanin ‘yan kasar milyan bakwai ne suka kada kuri’a a zaben. Ana sa ran za’a bayyana sakamakon zaben baki daya cikin watan gobe idan Allah ya kaimu. Za’a gudanar da zaben fidda gwani idan har babu wanda ya sami nasara kai tsaye cikin mutane takwas da suka yi takarar shugabancin kasar.
XS
SM
MD
LG