Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Biyu Sun Kamu da Cutar Polio A Najeriya


Bada allurar polio
Bada allurar polio

A Najeriya wasu kafofin yada labarai a kasar sun bada rahoton cewa mutane biyu sun kamu da cutar shan inna ko Polio a dai dai lokcinda kasar take shirin bikin cika shekaru biyar ba tareda an sami bullar cutar ba.

Jaridar Leadershgip yau Alhamis ta bada labarin cewa ministan kiwon lafiya na Najeriya yace gwamnati ta tura tawagar likitoci zuwa jahar Borno domin aikin rigakafi, inda nan ne cutar ta sake kunno kai.

Ministan kiwon lafiya Parfessa Isaac Adewole, ya kira lamarin koma baya, duk da haka yace "ina bada tabbacin ga kasana nan cewa zamu yi aiki tukuru na dakile wannan cuta," kamar yadda jaridar Leadership tay bayani. Ana sa ran gwamnati zata bada karin bayani kan barkewar cutar a wani lokaci yau Alhamis.

Cutar ta bulla ne a yankin da kungiyar Boko Haram take da karfi.A watan jiya kungiyar likitocin nan ta kasa da kasa da ake kira Doctors without Border da turanci ta kira matsalolin kiwon lafiya a jahar Barno da cewa "yana cikin yanayi mai tsanani" inda akalla mutane dubu dari biyar suke bukatar ruwa da abinci da muhallai da kulawa na gaggawa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG