Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 80 Ne Ruwan Sama Ya Rutsa Dasu A Japan


Barnar da ruwan sama ya yi a yankin Kurashiki, kasar Japan
Barnar da ruwan sama ya yi a yankin Kurashiki, kasar Japan

Sakamakon ruwan saman da aka dinga tafkawa kamar da bakin kwarya a Japan wanda ya kashe mutane 80 har yanzu ana neman ceto wasu da laka ta tafi dasu

Har zuwa cikin daren jiya Lahadi masu aikin ceto sun ci gaba da neman mutane da kwararowar laka a sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ta tapkawa ta rutsa dasu, harma ta kashe akalla mutane tamanin a kudu maso yammacin kasar Japan.

Fiye da mutane hamsin sun bace. Hukumar nazarin yanayi ta kasar ta gabatar da kashedi bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya a tsakiya da kuma yammacin kasar Japan ta hadasa kwararowar laka da batsewar rafi a yankin.

Prime Ministan kasar Shinzo Abe ya fadawa yan jarida cewa ana yunkurin ceto ba kama hannun yaro. Rabon da aga irin haka a kasar tun alif dari tara da saba’in da shidda, kimamin shekaru arba’in da biyu da suka shige.

An baiwa kimamin kusan mutane miliyan daya da rabi umarnin su fice daga gidajensu, yayinda aka sa kimamin miliyan uku cikin shirin kota kwana, kila suma a kwashe su daga gidajensu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG