Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 41 Sun Rasu Sanadiyar Ambaliyar Ruwa a Nijar


 Barnar Ambaliyan Ruwa
Barnar Ambaliyan Ruwa

Ruwa da aka tafka a Jamhuriyar Nijar kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyar ruguza muhallan dubban mutane tare da hallaka wasu 41 a sassa daban daban na kasar.

Kawo yanzu mutane 66,177 ne suka rasa muhallansu a Jamhuriyar Nijar sakamakon ambaliyan ruwa biyo bayan ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya.

Barnar Ambaliyan Ruwa
Barnar Ambaliyan Ruwa

Har wayau ambaliyar ta jawo mutuwar mutane kimanin 41 a sassan kasar daban daban kamar yadda daraktan hukumar ba da agajin gaggawa Kanar Bako Abubakar ya sanar.

Daraktan yana mai cewa a jihar Maradi mutane 22,988 al'amarin ya shafa yayinda mutane bakwai suka rasu. A Agadez mutane 593 ambaliyan ya shafa kana mutum daya ya hallaka. Sai yankin Diffa inda 1131 suka rasa muhallansu tare da mutuwar mutum daya. A jihar Doso mutum biyu ne suka hallaka sannan 21364 suka rasa matsuguninsu yayinda a jihar Tawa aka gano mutane uku da suka mutu kana 1508 suka yi hasarar muhallansu.

A cigaba da sanarwar Kanar Bako Abubakar ya ce a jihar Tilabery ma ambaliyar ta shafi mutane inda mutane uku suka kwanta dama yayinda 9501 suka yi hasara muhallansu. Sai jihar Zinder inda ruwan saman ya kashe mutane takwas ya kuma ruguza gidajen mutane 3934. A Yamai kuma, yankin da abun ya fi kamari mutane 16 suka kwanta dama yayinda aka gano mutane 8222 sun rasa gidajensu.

Ganin yadda lamarin ya kara rincabewa ya sa hukumomi suka kara daukan matakai lamarin da ya sa rundunar sojin sama ta bada izinin yin anfani da jirginta domin tantance zahirin halin da birnin Yamai ke ciki.

Sabon ruwan da aka tafka ranar Asabar ya sake ruguza wasu gidaje a birnin Yamai lamarin da ya tilastawa wasu mutane ficewa daga gidajensu suka nemi mafaka a makarantun boko kuma a cewarsu rashin mutunta tsarin gine gine ne ya kaisu ga wannan bala'in da tashin hankali. Mutane sun yi gine gine ba tare da barin magudanar ruwa ba.

Wadanda suka nemi mafaka a makarantun Boko sanadiyar ambaliyan ruwa
Wadanda suka nemi mafaka a makarantun Boko sanadiyar ambaliyan ruwa

Mutanen da abun ya shafa sun kira mahukumtar kasar da su taimaka masu.

Gwamnan Yamai ya ziyarci wuraren da ambaliyan ruwan ranar Asabar ya yiwa barna saboda haka yace zai yi bitar matsalar da ambaliyan ya haifar yau Litinin da yamma.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:37 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG