Mutane akalla 32 aka kashe a cikin tashe-tashen hankullan da suka barke a lardunan Oromia da Somali na kasar Ethiopia, wanda kuma akace kazamin fada ne da ya kaure tsakanin ‘yan kabilun Somali din da na Oromo, a cewar wani danmajalisar dokoki na kasar mai suna Boqor Ali Omar Aalle, wanda ya sheda wa Sashen Somaliyanci na VOA cewa mutanen 32 da aka hallaka sun hada harda kanensa da aka kashe a daren Litinin a a wani dan karamin gari da ake kira Awaday dake tsakanin Harar mai yawan Musulmi da kuma babban birnin nan na Dire Dawa.
Ko bayan danmajalisar, wasu kafofi da mutane da dama sun tabattarda barkewar wannan tashin hankalin, koda yake sunce kada a fadi sunayensu don suna tsoron a kawo musu farmakin ramuwar gayya. Sai dai har yanzu hukumomin kasar ta Ethiopia basu tabattarda gaskiyar rahottanin ba.
Facebook Forum