Lamarin ya auku ne a wata rugar Fulani da ke kauyen Gwanara da ke cikin karamar hukumar mulki ta Baruten a jihar Kwara, inda mutane 10 ‘yan gida daya suka rasa rayukan su, biyo bayan shan wani maganin gargajiya da aka jika a gidan.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu ba da maganin gargajiya 2; Okosi Musa da Worugura Junlin ne suka hada maganin, suka kuma baiwa wata mata ‘yar shekaru 40 da haihuwa mai suna Pennia Bonnie, sakamakon cutar da take fama da ita a tafin kafar ta.
To sai dai masu maganin sun shawarce ta da ta baiwa dukan iyalan gidan maganin su sha, domin kare su daga yaduwar cutar ta ta.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da aukuwar lamarin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Ajayi Okasanmi ya ce “wani mutum mai suna Ibrahim Bonie daga rugar Fulani a Gwanara, ya kai rahoton ga ofishin ‘yan sanda, cewa masu maganin gargajiya biyu sun je har gida suka baiwa mahaifiyarsa Pennia magani, domin cutar da ke kafarta.”
“Haka kuma sun umarce ta da ta tabbatar sauran iyalinta da ke gidan sun sha maganin, don kaucewa kamuwa da cutar,” in ji kakakin ‘yan sandan.
Okasanmi ya ci gaba da cewa “bayan da suka sha maganin ne sai mutanen gidan suka soma mutuwa daya bayan daya, inda kididdiga ta karshe, ta ba da adadin mutane 10 da suka mutu, ciki har da mahaifiyar da ke dauke da cutar ta kafa.”
Ya kara da cewa tuni da rundunar ‘yan sandan ta kama masu maganin biyu, kuma suna taimakawa ‘yan sanda wajen bincike da suke yi akan lamarin.
To sai dai ya yi kira ga al’umma da ke fama da rashin lafiya, da su rika neman magani a halatattun wurare da ke fadin jihar, domin kaucewa irin wannan “mummunan al’amari.”