A shirin mu na nishadi a yau alewa ce amma irin ta da, domin kuwa DandalinVOA yayin babban kamu inda muka samu bakunci Malam Habibu Sani Tudun wada, marubuci kuma mai shirya fina-finan Hausa.
Malam Habibu dai ya ce ya fara shirya fina-finai ne tun daga lokacin da aka fara wassanin dabe, har aka zo aka fara wassanin kwaikwayo yanzu ake fina-finai talabijin masu nisan zango.
Ya ce yana daga cikin mutanen da suka kafa Kannywood, inda suka fara da wassanin kwaikwaiyo a yunkurinsu na inganta al’adar Malam Bahaushe.
Ya kara da cewa kafin ya tsunduma ga harkar fim sai da ya shiga makarantar koyan shira fim a Jami’ar Bayero daga bisani ya tafi makarantar fim a garin Jos.
Ya ce abinda ya bambanta fina-finan farko da na yanzu dai ya danganci yadda aka bar al’ada aka kuma ari wasu bakin dabi’u da shirin tafiya da yadda zamani ta zo da shi.
Habibu ya ce babu abinda ba ya yi wajen baiwa marubuta da masu shirya fina finai shawarar wajen canza akalar yadda ake fim, ko da yake ya ce a yanzu sun fara hankalta.
Facebook Forum