Afurka ta samu gurbi biyu cikin jerin sunayen da mujallar Forbes ta bayyana na mata 100 mafiya shahara a duniya, wannan cigaba ne in aka kwatanta da na bara, Afurka ta samu gurbi daya tak.
Matan dai suna da alaka da siyasa da kuma diflomasiyya. Sun hada da Shugabar kasar Habasha Sahle Work Zewde, wadda a shekarar 2018 ma ita kadai ce ta kasance cikin jerin matan da aka sa sunayensu, sai kuma Amina Mohammed mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya daga Najeriya.
A shekarar 2017 mace daya da ta samu shiga shirin ita ce wata attajirar nahiyar Afurka kuma diya ga tsohon Shugaban kasar Angola, Isabel Dos Santos.
A 2016, Afurka ta samu gurbi 3, shugaban kasar Laberiya Ellen Johnson-Sirleaf, sai Shugabar kasar Mauritius sai kuma shaharriyar 'yar kasuwar nan ta Najeriya Folorunsho Alakija.
Mujallar ta Forbes ta ce mata a fadin duniya na ta kokari wajen ganin an yi gogayya da su a shugabanci, kasuwanci da kafafofin yada labarai, don haka ya dace kar a bar su a baya a wannan karon.
Facebook Forum