An zabi dan wasan gaba na kasar Masar mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Mohamed Salah a matsayin gwarzon shekara na Afrika 2018, bangaren maza.
Mohammad Salah, ya yi nasarar ne a kan takwararsa Sadio Mane dan kasar Senegal, wanda shima dan wasan Liverpool ne, da Pierre-Emerick Aubameyang na Gabon mai wasa a kungiyar Arsenal.
Karo na biyu kenan dan wasan na kasar Masar yana lashe kyautar a jere, shekarar 2017 da kuma 2018. Kuma shine ya kasance dan wasa na farko daga Arewacin Afrika da ya lashe kyautar sau biyu a jere.
Bikin karrama 'yan wasan tamola na Afrika ya gudanane ranar Talata 8 ga watan Janairun 2019 a kasar Senegal.
Sauran kyautukan da aka lashe sun hada da Gwarzuwa 'yar wasan kwallon kafa a bangaren mata Chrestinah Thembi Kgatlana 'yar Afrika ta Kudu.
Matashin dan wasa kuwa shine Achraf Hakimi mai taka leda a Borussia Dortmund dan kasar Morocco. A bangaren masu horaswa da kwallon kafa maza kuwa Herve Renard mai horar da Morocco shi ya lashe kyautar.
A mata mai horarwa Desiree Ellis ta Afrika ta Kudu ita ta samu nasara, bayan haka an zabi Tawagar kwallon kafa ta maza ta kasar Mauritania. Tawagar kwallon kafar mata ta Nigeria Super Falcons ce ta lashe kyautar.
Ita dai wannan kyautar wata Mujallar Kwallon Kafa ta kasar Faransa ce ta
fara bayarwa, a Afrika shekaru da dama da suka shude kafin daga bisani ta mika ragamar ga hukumar kwallon kafar ta Afrika ta CAF a wajejen shekarar
1990.
Facebook Forum