Akwai yar matsala a yaki da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, inji ministan tsaron Najeriya Janar Mansu Dan Ali.
Duk da matsalar da suke fuskanta sojoji ba zasu yi kasa da gwuiwa ba a kokarinsu na kakkabe burbushin 'yan ta'addan da ya ragu bayan da aka tarwatsasu a dajin Sambisa suka bazu wasu wuraren.
Janar Mansu Dan Ali, acewarsa suna iyakar kokarinsu domin ganin bayan kungiyar Boko Haram. Ya sake jaddada cewa sun ci karfinsu sai 'yan kalilan da suka saura da yanzu suke sauya salo. Ministan ya tabbatar da cewa zasu kara kaimi a wannan yakin da suka dukufa da kawo karshensa.
Ma'aikatar tsaro zata gudanar da binciken kwakwaf domin tabbatar da cewa babu wasu dake hada kai da 'yan ta'adda suna yiwa kasar zagon kasa. Binciken ya zama wajibi, inji minstan saboda yadda 'yan kungiyar ke yawan kai hare hare kwanan nan tare da yiwa sojoji kwantar bauna.
Daga bisani ministan ya yabawa 'yan jaridan jihar Borno game da sadakarwa da suka yi wajen bada sahihan labaru kan arewa maso gabashin kasar ba tare da son kai ba.
Shi ma gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya tofa albarkacin bakinsa yana mai cewa idan ba da 'yan jarida ba da tuni 'ya'yan kungiyar Boko Haram sun mamaye jihar gaba daya a shekarar 2013. Yan jarida ne suka ruwaita labarin cewa 'yan Boko Haram sun mamaye kananan hukumomin arewacin Borno lamarin da ya sa gwamnati ta wancan lokacin ta kafa dokar ta baci a jihohin Adamawa da Borno da ma Yobe. Matakin ne ya sa aka samu korar 'yan kungiyar.
A martanin da ya bayar shugaban 'yan jarida na jihar ya yaba da yadda abokanan aikinsa suka dukufa wajen fidda labaran abubuwan dake faruwa a jihar duk da cewa wasunsu sun rasa rayukansu sanadiyar yin hakan.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Facebook Forum