Kafin mika takardar tasa ya yi gargadi kan yadda komadar tattalin arziki da Lebanon ke fuskanta da rashin mayar da hankali wajen shawo kan wannan matsala, ka iya zama babbar barazanar da kasar ba ta taba gani ba tun bayan yakin basasan da aka yi.
A cikin wata sanarwa da Hitti ya fitar ya ce, "na lura cewa akwai ubanni gida da dama a kasata wadanda ke da ra’ayoyi masu karo da juna. Muddin ba su hada kansu don su ceci al’umar Lebanon ba, ba fata nake yi ba, kowa da kowa zai shiga uku."
Hitti ya kara da cewa, Lebanon na cikin hadarin zama "kasar da za ta zamanto komai ba ya aiki."
Babban jami'in diflomasiyyan ya zama ministan harkokin waje ne a watan Janairu a gwamnatin ta Firayim Minista Hassan Diab.
Rahotanin sun nuna cewar Hitti ya shiga yanayi na takaici ne sanadiyyar sukar da Diab ya yi ga Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Yves Le Drian, yayin wata ziyara da jami’in diplomasiyyan na Faransa ya kai Beirut a kwanan nan.
Sa'o'i kadan bayan Hitti ya ajiye aiki, shugaba Michel Aoun ya nada Charbel Wehbe a matsayin sabon ministan harkokin kasashen waje kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Facebook Forum