Rahotanni suna nuni da cewa masu arziki sun kara arzurta a wannan sabuwar shekarar 2015.
Hamshakin attajirin nan kuma mai ayyukan tallafawa al'umma Bill Gates yana ci gaba da rike matsayinsa na zama mutumin da yafi kowa kudi a duniya, matsayi da ya rike shekaru 16 cikin 21 da suka wuce. Kamar yadda mujallar Forbes ta yayi bayani jiya Litinin.
Bill Gates wanda yana cikin wadanda suka kafa kamfanin Microsoft arzikinsa ya karu da dala biliyan uku da miliyan dari biyu daga bara, wanda yasa arzikinsa ya kama Dala Biliyan $79 da miliyan dari biyu. Mujjalar tace banda haka Gates yayi kyautar wasu hanun jari na kamfaninsa kan kudi dala biliyan daya da rabi zuwa ga gidauniyarsa ta Bill and Melinda Gates.
Wanda ke binsa shine hamshakin atttajirin nan na kasar Mexico mai kamfanin hanyoyin sadarwa Carlos Slim Helu, wanda yake da dal biliyan 77 da miliyan dari.
Mujallar Forbes tace mutane metan da 90 suka shiga jerin wadanda arzikinsu ya kai biliyan cikin shekara daya data wuce. Kusan kashi 25 cikin dari na sabbin masu arziki da dukiyarsu ta kai biliyan a kasar China suke, kasar da inji mujallar take kan gaba da sabbin hamshakan masu kudi 71. Amurka ce ta biyu tana da mutane 57, sannan kasar India ta biyo bayada mutane 28, sai kuma kasar Jamus mai mutane 23.
Cikin sanannun mutane da suka shiga wannan jeri harda tsohon dan wasan kwando watau Basketball Michael Jordan, wanda ya cimma wannan matsaya saboda sayen wata kungiyar wasan kwallon kwando da ake kira Charlottes Hornets da kuma kudade da ya samu daga sayarda kayayyakin wasanni da sunansa a bangaren kamfanin Nike.