A karon farko dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Leonel Messi, ya bayyana cewa yana kishin abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo a gasar Laliga na kasar Spain.
Ronaldo ya yanke shawarar komawa kungiyar kwallon kafa ta Juventus ne, bayan ya ja ragamar Real Madrid wajan lashe kofin zakarun turai guda hudu cikin shekaru biyar.
Sai dai a kungiyar ta juventus ma tauraruwarsa taci gaba da haskawa, domin ko a kwanakin baya ya tallafa mata, inda ya zurara kwallaye uku a ragar Atletico Madrid cikin gasar cin kofin zakarun Turai (Uefa) zagaye na 16, wanda hakan yasa Juventus ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin wasan daf da na kusa da na karshe.
Messi yace yayi bakin cikin rashin sa saboda babban dan wasa ne duk da cewa banason na ga yana lashe kofi a lokacin da yake kungiyar Real Madrid, amma komawar sa Juventus ta samu kwarin gwiwa da zata iya lashe kofin zakarun Turai.
Messi ya ce duk da cewa akwai manyan 'yan wasa a duniya irinsu Neymar, Mbappe, Suares da Sergio Aguiro, sai dai yace ya ambaci Ronaldo ne domin shine matakinsu daya a bangaren kwararru.
Facebook Forum