Mahaifin Leah Sharibu, ya bayyana cewa bashi da tabbacin sahihancin rahoton da aka yayata a wadansu jaridun Najeriya, da ke cewa Leah ta haifi da namiji bayan Musuluntar da ita da kuma yi mata auren dole da wani kwamandan kungiyar Boko Haram ya yi.
A cikin hirarshi da Sashen Hausa, Nathan Sharibu ya ce kawo yanzu, babu wata hukuma da ta tuntube shi dangane da Leah, saboda da haka bashi da wani bayani game da rahoton da ya karanta a yanar gizo.
Leah Sharibu, ita ce yarinya daya tilo da ta rage a hannun kungiyar Boko Haram, daga cikin ‘yan makarantar sakandaren Dapchi dari da goma da kungiyar Boko Haram ta sace ranar goma sha tara ga watan Fabrairu shekara ta dubu biyu da goma sha takwas a lokacin tana da shekaru goma sha hudu.
Kungiyar ta saki sauran ‘yan mata dari da hudu da suka rage da rai, amma ta ci gaba da garkuwa da Leah saboda da taki musulunta.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha nanata niyar gwamnatinsa ta ceto Leah da kuma sauran mutanen da kungiyar Boko haram ke garkuwa da su.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Facebook Forum