Kasa da mako guda kafin babban zaben da za a yi a Najeriya, har yanzu babu dan takarar gwamna da jam’iyyar APC ta tsayar a jihar Zamfara.
A kuma karon farko, shugaban Najeriya ya yi tsokaci kan wannan dambarwar siyasa da ta sa wasu kotuna biyu suka ba da hukunce-hukunce masu karo da juna.
“Duk gardamar da ake yi, yana wurin shari’a, za mu dakata, amma idan Allah ya yarda, daga yau kafin Asabar mai zuwa a fara zabe, ita hukumar zabe za ta fadi wanda ta yarda da shi.” Inji Buhari a lokacin da yake jawabi a yakin neman zaben da yaje jihar jiya Lahadi.
Ba kamar yadda ya saba ba a jihohin da ya je yakin neman zaben, shugaba Buhari bai daga hannun kowa a matsayin wanda za a zaba gwamna a jihar ba.
A kwanakin baya ne wasu kotuna biyu suka ba da hukunce-hukunc masu karo da juna kan takaddamar ‘yan takarar.
Wata babbar kotu a Gusau ta yanke hukuncin cewa an yi zaben fidda gwaman na ‘yan takara a jam’iyyar, lamarin da ya yi hannun riga da matsayar da hukumar zabe ta INEC ta dauka.
Baya ga haka wata kotun tarayya a Abuja kuma, ta yanke hukuncin cewa ba a yi sahihin zaben fidda gwani ba, saboda haka jam’iyyar ba ta da damar fitar da dan takara.