Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Ce Za'a Kawo Karshen Cutar Sida A Shekarar 2030


Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres

Shugaban hukumar dake yaki da sida ko HIV/AIDS na Majalisar Dinkin Duniya, Michael Sidibe ya ce an kai wani muhimmin mataki a yaki da cutar kuma za'a kawo karshenta a shekarar 2030

Shugaban hukumar da ke yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDS a Majalisar Dinkin Duniya, Michel Sidibe, ya ce an kai “wani muhimmin mataki” a yunkurin da ake yi na kawo karshen wannan bala’i nan da shekarar 2030.

A wata hira da ya yi da Muryar Amurka, Sidibe ya ce, “tsakiyar wa’adin kawar da wannan cuta na da matukar muhimmanci, domin mataki ne da za mu yi waiwaye mu ga abin da ba ya tafiya daidai,” yana mai cewa wannan shekarar ita ce tsakiyar wa’adin da kasashen duniya suka shata na kawar da cutar, “kuma an fi maida hankali ne akan yankunan da wannan cuta ke saurin tasari akansu.”

Kididdigar da aka yi a shekarar 2016, ta nuna cewa, akalla mutum miliyan 36.7 ke dauke da kwayar cutar ta HIV.

Sannan an samu kusan mutum miliyan biyu a matsayin sabbin wadanda suka kamu da cutar, kana mutum miliyan daya suka mutu daga cutar.

Abin farin cikin a nan, kamar yadda kididdigar ta nuna, shi ne, an yi nasarar fadada hanyoyin samun magungunan da ke rage kaifin cutar, inda kusan mutum miliyan 21 suka samu magungunan a shekarar 2016, lamarin da ya sa aka samu raguwar mutanen da ke mutuwa daga cutar ta AIDS da kashi daya cikin uku.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG