Babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya Air Marshall Sadique Abubakar yace jiragen leken asirinsu sun gano yunkurin wasu mayakan Boko Haram na sake kafa sabbin sansanoni a dajin Sambisa.
Sun gano wurare guda hudu da yan ta'addan ke akai, dalilin ma kenan da yasa suka kaddamar da shirin sintirin OPERATION RUWAN WUTA a wannan dajin.
Air marshall Sadique Abubakar yace sojojin saman sun sami nasarar ragargaza yan ta'addan kuma a halin yanzu suna nan suna ta sintiri a duk sassan dajin na Sambisa don tabbatar da kare dukiya da rayukan yan Najeriya,
Babban hafsan hafsoshin sojojin saman yace sunyi ruwan wuta na kimanin kwanaki goma kuma kwalliya ta biya kudin sabulu, yana mai
cewa suna yin taka tsantsan a wannan yaki da akeyi da ta'addanci don
gujewa afkawa wadanda basu jiba basu ganiba,kamar yadda yace
''AL'AMARIN YAKI A SAMA YANA DA WASU KA'IDODI, WANDA DAYA DAGA CIKI BA KO DA YAUSHE BANE ZAKAGA MUTANE KAWAI KA AFKARMASUBA, DOLE KA TABBATAR MUTANEN DA ZAKA AFKAWA SUN CANCANCI A AFKA MASUN, DAN AINIHIN ABIN DA YASA MUKE WANNAN YAKI SHINE MU KARE MUTUNCIN MUTANE, WANDA BASIJI BA BASU GANI BA AKE YAYYANKASU BISA ZALUNCI, SABODA HAKA IN CIKIN YIN HAKA KUMA KAJE KA AFKAWA WANDAI BAI DA WANI HAKKI A CIKI KAGA KAIMA KA FADA SAHUN SU KENAN, DON HAKA MUKE DAUKAR LOKACI DON TACE DUK ABUBUWAN DA MUKA GANI DON WANNAN OPERATION YAYI NASARA,''
Tsohon kwamanda a rundunar sojin saman Najeriya Air Commodore Ahmed Tijjani Baba Gamawa yace yana da kwarin gwuiwar wannan sintiri na OPERATION RUWAN WUTA zai yi nasara sosai domin yanzu duk duniya sojin sama ne ke jagorantar duk wasu yake yake
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum