Mutanen sun rasu ne a wadansu hare hare dabam dabam da aka kai jiya Litinin.
Jami’an tsaro sun ce ‘yan bindigan sun harbe tsohon babban kwanturolan gidan yarin Ibrahim Jarma a arewacin jihar Bauchi.
Hukumomi sun ce an kaiwa Jarma hari ne bayan sallar la’asar a wani masallaci dake kusa da gidansa a garin Azare.
A jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, jami’an gwamnati sun ce wadansu mutane dake dauke da makamai sun kaiwa lauyan gwamnatin jihar Zanna Malam Gana hari a cikin gidansa dake garin Bama.
Kungiyar mai tsatsauran ra’ayin addini dake da cibiya a jihar Borno bata dauki alhakin kisan mutanen biyu ba.
An kai hare haren ne ‘yan sa’oi bayanda dakarun Najeriya suka yi ikirarin cewa, sun kashe wani da ake kyautata zaton kakakin kungiyar Boko Haram ne, mai lakabi Abul Qaqa. Babu tabbacin cewa, an kashe kakakin kungiyar.