Duk da irin taskun da masu yin fina-finai suka shiga a Jihar Kano, Sakna Gadaz tana daya daga cikin mawaka, kuma jaruman fina-finai kalilan dake ganin cewa wannan harka ta fina-finai tana bunkasa cikin jihar, maimakon ja da baya da wasu ke zato.
Ita dai Sakna Gadaz, haifaffiyar unguwar nan ta Sharada a Kano, ta fara ne da wakokin Islamiyya a shekarar 2000, daga nan ta koma ga wakokin fina-finai, har ta zama jaruma kuma fardusa ta fina-finan Hausa. Ta fadawa filin "A Bari Ya Huce..." cewar a yanzu an samu gyara sosai cikin harkar fim a Kano, abinda ta ke ganin zai kara bunkasa wannan harka, duk da cewa akasarin masu yin fina-finan sun tare zuwa Kaduna da wasu wurare a saboda abinda suka kira shisshigi da tsangwamar da ake yi musu.
Sakna Gadaz dai ba wai wakoki da fina-finai kawai ta sanya a gaba ba, domin kuwa ta kammala karatunta na babban difloma, watau HND, kuma tana shirin tafiya aikin hidimar kasa (NYSC).
A cikin kashi na farko na tattaunawar, za a ji tarihin wannan jaruma har zuwa fara wakokinta. A kashi na biyu dake tafe za a iya jin yadda ta shiga fina-finai da kuma abubuwan da ta sanya a gaba a yanzu.