Matsayin kungiyar kwallon kafa ta Kasar Ivory Coast, ya cira sama bayan da ta cinye gasar kofin kwallon kafa na nahiyar Afirka, wadda kasar Equatorial Guinea, ta karbir bakunci.
A jerin kasashe goma, da suka fi a wasan kwallon kafa, kasar Algeria, ce take kan gaba sai kuma zakarun bana, wato Ivory Coast, wace ta zo ta biyu a nahiyar Afirka, inda kasar Ghana, ke biye da ita, Tunisa ce ta hudu.
Kasar Cape Verde, ita ke ta biyar, sai dogaye iya tafiya, Senegal, wace ta kasance ta shida, ita kuwa Najeriya, warwas tayi ta koma ta bakwai, koda yake rashin tabuka abun arziki a faggen wasan kwallon kafa, ya hana ta shiga gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar.
Guinea, ta haye mataki na takwas, kamaru, ce ta tara, ita kuwa kasar Congo ta goma.
A duniya kuwa ga yadda suke , kasar Jamus, ce ta daya, Argentina, ta biyu, Columbia,ta uku, Belgium, ta hudu kasar Netherlands wato Holland ta zo ta biyar.
Sauran su hada da Brazil, ta shida, Portugal ta bakwai, ita kuwa kasar Faransa ta takwas, Uruguay ta tara, kasar Spain ta kasance ta goma.