Laraba ne wani mutum mai suna Nura Iliyasu mazaunin Kaduna ya tafi Abuja da wani irin salon zanga zangar kin manufofin gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari inda ya hau turken salula dake bayan fadar Aso Rock ya kuma yi alkawarin yin kwana bakwai ba tare da cin abinci ba sai dai shan ruwa.
Yau ya sauko ya na cewa "wasu mutane 'yan kalilan sun mallake dukiyar Nigeria kuma gasu nan sun fi karfin doka".
Nura Iliyasu wanda ya sauko yinda ya shiga yini na biyu akan turken ya ce Nigeria ce ta shida mafi arzikin man fetur a duniya amma ba ta da matatar mai daya rak dake aiki.
Mutumin wanda yake rike da robar ruwa da zai dinga sha cikin kwanaki bakwan da ya kuduri kasancewa a kan turken tun farko, ya bukaci 'yan adawa su fitar da dan takara na nagari. Ya caccaki gwamnatin Buhari da cewa ta gaza.
Nura Iliyasu ya sauko ne bayan sharadin sai wakilin Muryar Amurka ya kasance a wurin domin tattaunawa dashi. Ya kira wakilin na Muryar Amurka ya fada masa cewa akwai wakilin CNN amma ya bukaci ya tuntubi shi wakilin na Muryar Amurka.
Kafin zuwan sa daga Kaduna ya fadawa Sashen Hausa cewa shi ya na cikin hankalinsa, bugu da kari kuma shi mahaddacin Kur'ani ne. Ya ce shi mutum ne mai sana'a wanda yake da ilimin boko da na addini.
Yace ya dauki wannan matakin ne saboda halin da 'yan Nigeria ke ciki. Yace shugabannin kasar suna bukatar a duba hankalinsu. Yace kowa"zai zo da romon baka ya ce ya fi kowa gaskiya. Ya na hawa sai ka ga akasin haka, sai ka ga gwanda ma wanda ya sauka..."
Ya kuma ce"bai gamsu ba, da mulkin Buhari ba, ba kuma zai gamsu ba saboda bai ga alamar abun da zai gamsar da shi ba"
Ana cikin zantawa dashi sai jami'an tsaron farin kaya DSS suka yi awan gaba dashi cikin wata mota. Haka ma sojoji suka yi dafifi a wurin duk da cewa matashin ya dage akan cewa ba 'yan siyasa suka tunzurashi ba.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Facebook Forum