Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matashi Yayiwa Banki Fashi Amma Yace Bai Aikata Laifi Ba


A bank teller counts a stack of US and Chinese currency.
A bank teller counts a stack of US and Chinese currency.

Wani matashi da ake zargi yayi wa banki fashi ya amince kan cewar ya ‘dauki makurden kudade daga bankin, yakuma ‘dauki hotan bidiyon fashin harda saka shi shafin sadarwa na yanar gizo – amma fa yace shi bai aikata laifi ba domin ya tambayi kudin cikin ladabi.

Dominyk Antonio Alfaonseca mai shekaru 23 da haihuwa yace, abinda yayi ranar litinin da yamma bai kamata ba ace an dauke shi a matsayin fashi da makami, saboda ya rubuta sako cikin takarda ya kuma mikawa ma’aikaciyar bankin TowneBank dake jihar Virginia, sakon ma ya kare da alamar murmushi.

A wata hira da ma’akacin gidan talabishin na NBC yayi da wannan matashi a gidan kaso, yace “fashi da makami dai shine ka nemi abu a hannun wani kuma ka karbe abinda ka nema kamar kudi da dai sauransu. Amma ni banyi haka ba.”

ya dai ‘dauki rubutaccen sakon daya mikiwa ma’aikaciyar bankin ya kuma kafe kan shafin sa na Instagram kamar haka, “Ina bukatar dala dubu dari da hamsin yanzunnan!! Don Allah.”

Sakon ya cigaba da cewa “zai ‘dauki ‘yan sanda mintuna 3 zuwa 4 su zo nan. Ina mai matukar godiya idan kika dannan kararrawa bayan na tafi…..ki kuma tabbatar baki saka fasahar nan da banki ke amfani da ita ba wadda ke saka maki a takardun kudi :-)”

‘yan sanda dai basu yarda da bayanin Alfonseca ba, sun ma kameshi mintuna 20 bayan da yayi fashin ‘dauke da jaka cike da kudi, an kuma kaishi gidan kaso. Za kuma a gurfanar da shi gaban alkali 12 ga watan Yuni.

XS
SM
MD
LG