A ranar Litinin 7 ga watan Afirilun 2019, aka kammala gasar karshe na wasan tebur wato 'TableTennis', a turance na masarautar Yauri (Yauri Emirate Council) dake Jihar Kebbi a tarayya Najeriya.
Ita dai wannan gasar itace karo na farko da aka tabayi wanda ta samu halartar 'yanwasa guda 15 daga Kananan hukumomi uku da suke kar kashin masarautar Yauri, inda aka shafe mako guda ana fafatawa.
Wasan karshen ya samu halartar wakilin Maimartaba Sarkin Yauri, Alh Aliyu Muhammad Gado, sai wakilin Fagachin Yauri Alh Bala Gagga, wanda kuma Shugaban wasan kwallon teburin na masarautar Yauri, da Alh Hussain Umar, Alh Aliyu Danmutun, akwai Alh Yusuf Alasan, Alh Abdullahi Apasco dadai sauran jama'a, wanda ya gudana a Tashar Garkuwa.
Angudanar da gasar har kashi uku, an nemi na hudu, uku, biyu da na daya.
Wanda ya samu nasarar lashe gasar a mataki na daya shine Raymond, inda ya samu kyautar kudi naira dubu dari, na biyu Garba Garus, sai Akure da ya zo na uku inda dukansu suka samu kyauta ta musamman.
Facebook Forum