Inji Kaigama shugaban wata kungiyar matasan Diffa ya ce kowane irin harkar kasuwanci da aikin yi ya tsaya cik a yankin Diffan.
Da can harkokin babura da motoci ko su sayar ko kuma su yi aikin daukan fasinjoji dasu suka saba yi. Yawan hare haren Boko Haram ya sa aka tsayar da sayar ko daukan fasinjoji da babura.
Sun koma aikin jigilar fasinjoji zuwa Agadez daga can kuma zuwa Jado. Kafin a dakatar da jigilar fasinjojin sukan samu mutane dari takwas kowace rana.
Akan yin zirga zirga daga Diffa zuwa wasu garuruwan Najeriya, Kaigama ya ce akwai hatsari shiga garuruwan saboda matsalar Boko Haram da kuma tsadar rayuwa. Ya ce harkar Boko Haram ce ta karya masu baya ta kawo cikas a koina, tattalin arzikinsu ya komade.
A cikin Diffan kanta duk wasu ayyuka da ake yi dake samar ma matasan aikin yi su ma sun tsaya. Mutanensu dake Jado an korosu sun dawo sun hadu da wadanda suke gida suna zaman kashe wando.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani
Facebook Forum