Kungiyoyi da daidaikun ‘yan Nijeriya na cigaba da yin amfani da damar da dage lokacin zabe ya haifar wajen fadakar da matasa da sauran ‘yan Nijeriya muhimmancin kada kuri’a ranar zabe da kuma zaben nagari.
Da ya ke bayani ga wakilarymu Baraka Bashir, Sakataren hadakar kungiyoyin matasa (Coalition for Northern Youths) Malam Haruna Dahiru Bindawa ya ce kungiyarsu ta ma ji dadin dage zaben saboda dagewar ta bas u damar fadakar da jama’a musamman ma matasa. Ya ce ko a zabukan baya ma sun yi amfani da zarafin da su ka samu wajen fadakar da matasa kan illar tashin hankali a lokacin zabe. Y ace sun nuna ma matasa cewa idan sun lura masu baiwa matasa kudi su yi shaye-shaye bas u yadda nasu ‘ya’yan su shiga bangar siyasa saboda hakan ba sana’a ce ta mutunci ba.
Alhaji Bindawa y ace tuni Kudancin Nijeriya ya yi ma arewaci fintinkau ta dukkannin fannonin cigaba saboda rashin alkibla mai kyau da matasan arewa ke bi. Hasalima, in ji shi, duk wata kasa ko al’ummar da ta cigaba, to matasa ne sanadi kuma su ne sanadin akasin hakan. Don haka y ace sun a zagaya jiha-jiha su na fadakar da matasa kuma idan Allah ya yadda za a sami saukin matsalar bangar siyasa.