Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa ku Sani Bangar Siyasa Bazata Haifar da Da Me-Ido Ba


YALI
YALI

Wasu matasa masu kishin kasarsu Nijeriya, da suka samu horas wa a jami’o’in Amurka a shekarar da ta gabata, a wani kwarya kwaryar horaswa da shugaban kasar Amurika Barak Obama, ya kirkiro, don bama matasan Afrika damar fahimtar me duniya ke ci a fannoni daban da ban. Sun gudanar da wata lakca a dakin taro na tsangayar shari’a a jani’a Bayaro da ke kano.

Wannan taron kwana daya me taken, Matasa ku fuskanci cigaban kasar ku, wanda malamai da dama sun halarci wannan taron kuma sun gabatar da kasidu, daya dagacin magabata a wannan taron Barista. Safiya Ahmad Nuhu, tayi muna Karin haske dangane da wannan taron.

Tace wannan taron ya meda hankali ne akan matasa, ganin cewar zabe na kara karatowa a kasar, wannan yasa suka ga akwai bukatar su wayar ma matasa da kai akan bangar siyasa. Tace a shekarar da ta gabata sun halarci wani horaswa a kasar Amurika, inda suka ga yadda ake gudanar da shugabanci mai adalci da tsarin siyasa, wannan yasa suka ga yakamata su yi wannan taron karama juna sani don su wayar ma matasa da kai akan bangar siyasa.

A cikin wadanda suka gabatar da kasidu, sun yi magana kwarai akan matasa su guji bari ayi amfani dasu don tada zaune tsaye, suma ‘yan siyasa su sanifa idan bazasuyi ma kawunansu abuba, to kada suyi ma yayan wasu. Don haka suna kara kira da matasa su fita kwansu da kwarkwatar su ranar zabe su kada kuri’ar su kuma su guji duk abubn da zai kawo rashin jituwa a tsakanin su da malaman zabe. Haka kuma suma jami’an tsaro su guji yin amfani da karfi don cin zarafin 'yan kasa a lokacin zaben.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG